logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya gabatar da muhimmin jawabi a bikin bude taron dandalin tattaunawa kan ci gaban kasar Sin na shekarar 2024

2024-03-24 17:12:14 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya halarci bikin bude taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa kan ci gaban kasar Sin na 2024, tare kuma da gabatar da muhimmin jawabi a yau Lahadi, 24 ga wata a nan birnin Beijing.

A yayin jawabinsa, Li Qiang ya bayyana cewa, yanayin farfadowar tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da karfafuwa, kana sabbin masana’antu, sabbin samfura da ma sabon karfi, na samun saurin karuwa, yana mai cewa ta hakan za a iya gano cewa, kyakkyawan yanayin tattalin arzikin kasar Sin mai matukar juriya da kyakkyawan makoma, kuma mai cike da kuzari, ba zai canza ba.

Firaministan Li ya kuma bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin a yau ya hade sosai da tattalin arzikin duniya. Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da kirkirar yanayin kasuwanci na kasa da kasa mai dacewa da kasuwa da dokoki wadanda ke matsayin gaba a duniya, da zurfafa gyare-gyare a wasu muhimman fannoni da hanyoyi, za kuma ta ci gaba da hada duniya ta hanyar bude kofa bisa babban matsayi.

A cewar firaministan Li, ko shakka babu kasar Sin mai karfafa bude kofa za ta kawo karin damammakin hadin gwiwa da samun nasara tare ga duniya. Haka kuma, kasar Sin na son gabatar da manyan damarmakin da ta samu wajen samun ci gaba mai dorewa ga duniya, da yin aiki tare da bangarori daban daban don kafa wata makoma mai kyau ta samun bunkasuwa tare.

An bude taron dandalin tattaunawa kan ci gaban kasar Sin na shekarar 2024 ne a yau Lahadi da safe a birnin Beijing, wanda za a shafe kwanaki biyu ana yinsa, babban taken taron shi ne “Kasar Sin dake samun ci gaba mai dorewa”. Jami’an da suka fito daga wasu muhimman kungiyoyin kasa da kasa da manyan masana’antu 500 da suka yi fice a duniya, da ma shahararrun kwararru da dama a duniya, za su tattauna tare da cudanya kan batutuwa da dama, ciki har da ci gaban kasar Sin mai dorewa da dai sauransu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)