logo

HAUSA

Kungiyar CEDEAO ta yi allawadai da babbar murya da harin ta’addancin da ya kashe sojojin Nijar 23

2024-03-24 16:40:01 CMG Hausa

A ranar jiya Asabar 23 ga watan Maris, kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta CEDEAO ko ECOWAS ta fitar da wata sanarwa domin jajantawa kasar Nijar bisa ga harin ta’addancin ranar Laraba 20 ga wata da ya yi sanadiyar mutuwar sojojin Nijar da dama.

Daga birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, wakilinmu, Mamane Ada ya aiko mana da rahoto kan wannan sakon ta’aziyya na CEDEAO.

Sakon na cewa, tare da bacin rai da kaduwa ne kungiyar CEDEAO ta samu labarin mutuwar sojojin Nijar 23 a cikin wani kwanton bauna na ‘yan ta’adda a lokacin da sojojin suke aikin sintiri da kakkaba a yammacin kasar, kusa da iyaka da kasashen Mali da Burkina Faso.

A wannan lokaci na juyayi da bakin ciki, gamayyar kungiyar cigaban kasashen yammacin Afrika CEDEAO na aika ta’aziyyarta ga gwamnatin Nijar da al’ummar Nijar baki daya, da kuma bayyana goyon bayanta ga iyalan mamatan da kuma rundunar sojojin kasar Nijar. Haka kuma, kungiyar CEDEAO na yin tir da allawadai da babbar murya da wannan hari, tare kuma da tabbatarwa hukumomin Nijar da goyon bayanta na hada karfi da karfe domin yaki da ta’addanci da kuma da kaifin kishin addini a cikin yankin Sahel.

A ranar Laraba 20  ga watan Maris din shekarar 2024, sojojin FAN suka ci karo da wani harin ‘yan ta’adda a kewayen kauyen Teguey da cikin jihar Bankilare, yankin Tillabary, wanda yayi sanadiyar mutuwar sojojin Nijer 23 da raunata 8, yayin da a bangaren abokan gaba aka kashe ‘yan ta’adda kusan 30 da kuma kwace makamai da kayayyakin yaki da dama, a cewar sanarwar rundunar sojojin Nijar. (Maman Ada)