logo

HAUSA

An kaddamar da zaben shugaban kasa a Senegal

2024-03-24 20:39:39 CMG Hausa

An kaddamar da zagaye na farko na zaben shugaban kasa a kasar Senegal da misalin karfe 8 na safiyar yau Lahadi, agogon GMT.

Bisa kididdiga daga hukumar zabe ta kasar, ana sa ran kimanin masu kada kuri’a miliyan 7.37 ne za su zabi shugaban kasar na 5. Daga cikin adadin, sama da miliyan 7 na cikin kasar yayin da ragowar ke kasashen ketare.

‘Yan takara 19 ne za su fafata a zaben domin maye gurbin shugaba mai barin gado Macky Sall, wanda aka zaba karon farko a shekarar 2012, sannan aka kuma sake zabensa a shekarar 2019. (Fa’iza Mustapha)