logo

HAUSA

Batutuwan diflomasiyya da aka amincewa yayin taron birnin Beijing sun haskaka ma’anar dimokaradiyya

2024-03-23 15:36:27 CMG Hausa

A baya bayan nan, yayin dandalin tattaunawa kan dimokaradiyya na kasa da kasa karo na uku, mai taken “Dimokuradiyya, darajar dan Adam ta bai daya” wanda ya gudana a birnin Beijing, sama da mahalarta 200 daga kasashe da yankuna, da hukumomin kasa da kasa sun zurfafa tattaunawa, game da muhimman batutuwa da suka hada da "Dimokaradiyya da zamanantar da jagoranci", da jigon "AI da makomar dimokaradiyya", da "Dimokaradiyya da jagorancin duniya, a yanayi na tasirin mabanbantan sassan duniya".

Matsaya guda da aka cimma tsakanin mahalarta taron, ita ce fatan da ake son cimmawa game da dimokaradiyya bai wuce karewa, da kuma kyautata rayuwar bil adama ba. Mahalarta taron na ganin wajibi ne a martaba ‘yancin al’ummun dukkanin kasashe, na zabar turbar su ta neman ci gaba, kana a kauracewa amfani da dimokaradiyya a matsayin makamkin rarraba kawuna, da yada kiyayya, da gurgunta zaman lafiya tsakanin sassan kasa da kasa.

Kusan a lokaci guda, ita ma Amurka ta gudanar da taro na 3 na "Raya dimokaradiyya", wanda ta dauki nauyi da hadin gwiwar Koriya ta kudu, wanda kuma bai yi wani armashi ba. Tun daga yadda aka yayata taron har zuwa rashin samun karbuwarsa, taron na "Raya dimokaradiyya" da Amurka ta tsara, ya fayyace ainihin rashin gaskiya dake tattare da salon dimokaradiyyar Amurka.  (Saminu Alhassan)