logo

HAUSA

Ya kamata Amurka ta yiwa duniya bayani game da matsalolin da jiragen kamfanin Boeing ke fuskanta

2024-03-23 15:51:18 CMG Hausa

A baya bayan nan, Amurka ta kasa zaune ta kasa tsaye, tun bayan da jama’a suka fara bayyana mabanbanta ra’ayoyi, don gane da matsalolin da jiragen sama kirar kamfanin Boeing na Amurka ke gamuwa da su.

Daga karshe dai, wani babban jami’in kasar ya amince cewa, akwai wasu batutuwa masu alaka da matsayin ingancin jiragen kamfanin na Boeing. Sai dai duk da haka, ba a samu wasu gamsassun bayanai, game da hanyoyin magance matsalolin daga bangaren waje, da bangaren hukumomin gwamnati masu sanya ido a fannin ba.

Tun daga farkon shekarar nan, jiragen kamfanin Boeing sun rika gamuwa da matsalolin daka iya haifar da hadari. A cewar kafar watsa labarai ta “Fox News” dake Amurka, tsakanin watan Janairu zuwa Fabarairu kadai, jiragen sama kirar kamfanin Boeing sun gamu da hadurra har sau 6. Kaza lika a watan Maris, jiragen kamfanin sun fuskanci matsaloli da dama, ciki har da na fitar taya yayin tashi, da gobarar inji yayin da yake sama, da rashin wasu sassan jikin jirgi.

Masharhanta na ganin matsalolin kira na jiragen kamfanin Boeing na da dadadden tarihi, kuma rashin ka’idojin sanya ido daga tsagin hukumomin gwamnatin Amurka masu ruwa da tsaki, na kan gaba wajen dorewar matsalolin da jiragen kamfanin na Boeing ke fuskanta. (Saminu Alhassan)