logo

HAUSA

Kutsen bangaren Philippine a tudun Ren'ai ba zai haifarwa kasar ‘da mai ido ba

2024-03-23 16:28:35 CMG Hausa

Kakakin rundunar tsaron yankunan teku na Sin Gan Yu, ya ce a yau Asabar 23 ga wata, bangaren kasar Philippines ya keta alkawarin da ya yi, ya sake aikewa da jirgin ruwan dakon kaya daya, da na dakarun tsaron teku biyu, ba tare da amincewar bangaren kasar Sin ba, zuwa daura da sashen tudun ruwa na Ren'ai, wanda ke karkashin tsibiran Nansha mallakin kasar Sin.

Gan Yu, ya ce bangaren Philippines ya yi kokarin aikewa da kayayyaki ne, ciki har da na gine gine, zuwa babban jirgin ruwan da kasar ta girke ba bisa ka’ida ba a sashen tudun ruwa na Ren'ai.

Jami’in ya ce bangaren dakarun tsaron teku na Sin ya yiwa jiragen na Philippines gargadi, yayin da suke tunkarar wuraren da suka sabawa doka, amma duk da haka, jiragen na Philippines ba su dakata ba. Ya ce ‘yan sandan teku na Sin sun aiwatar da dokoki, sun tsare jiragen ruwan, sun kuma juyar da su baya, bisa tanadin doka da ka’idoji tabbatattu.

Gan Yu ya kara da cewa, "Mun gargadi bangaren Philippine da cewa, wanda ya yi wasa da wuta zai jawowa kan sa jin kunya. ‘Yan sandan tsaron teku na Sin har kullum a shirye suke, za kuma su tabbatar da tsaron ikon Sin na mallakar yankunan ta, da hakkokinta na teku". (Saminu Alhassan)