logo

HAUSA

Bola Ahmed Tinubu: Tabbas wadanda suka hallaka sojoji a Delta za su fuskanci hukunci mai tsanani

2024-03-23 14:43:37 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa, gwamnati za ta zartar da hukunci mai tsananin gaske kan mutanen da suka hallaka sojoji a jihar Delta.

Ya tabbatar da hakan ne, lokacin da yake jagorantar taron shan ruwa na musamman da ya shiryawa shugabannin majalissar dattawan kasar a fadarsa dake birnin Abuja, inda ya ce, irin danyen aikin da wasu al’umomin jihar Delta suka aikata ba za a taba yin hakuri a kansa ba .

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoton. 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce, gwamnati ba za ta amince wasu marasa kishin kasa su ci gaba da daukar doka a hannunsu ba, inda ya ce yana daga cikin manyan ayyukan ta’addanci kai farmaki ga masu kare kasa daga abokan gaba.

Shugaban na tarayyar Najeriya ya ci gaba da cewa, Najeriya kasa ce mai cikakken iko wadda take da damar kare martabarta a kowanne mataki.

Ya tabbatarwa sojojin kasar cewa, za su ci gaba da samun hadin kai da goyon bayan gwamnatinsa a aikin da suke yi na kare kasar daga barazanar tsaro da take fuskanta.

“Dakarun sojinmu suna aiki tukuru, a don haka ba za mu bari mahara su keta mutunci da kima su ba tare da jagororinsu, za mu ci gaba da ba su kwarin gwiwa wajen tabbatuwar kasa mai ’yanci tare da kare hakin ’yan kasa kana da fatattakar talauci a tsakanin al’ummarmu.”

Idan dai za a iya tunawa a kwanakin baya ne wasu matasa ’yan ta’adda dake cikin al’ummar Okuama a jihar Delta suka yiwa wasu dakarun sojin Najeriya su 17 kisan gilla yayin da suke tsaka da aikin tabbatar da zaman lafiya a yankin. (Garba Abdullahi Bagwai)