logo

HAUSA

Ministan ma’aikatar ciniki na Sin ya gana da shugaban kamfanin Apple

2024-03-23 20:13:57 CMG Hausa

Ministan ma’aikatar ciniki na Sin Wang Wentao, ya gana da shugaban kamfanin Apple Tim Cook a jiya Juma’a.

Yayin ganawar ta su, mista Wang ya ce hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka na haifar da daidaito a fannin raya alakar sassan biyu. Kaza lika, Sin a shirye take ta yi aiki tare da Amurka wajen samar da yanayin adalci, madaidaici, na hadin gwiwar kamfanonin kasashen 2.

Yayin zantawar jami’an biyu, sun kuma yi musayar ra’ayoyi don gane da batutuwa masu yawa, ciki har da bunkasar hada hadar kamfanin Apple a Sin, da kuma alakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka.

A tsokacin da ya gabatar, mista Cook ya ce Sin muhimmiyar kasuwa ce, kuma jigon rarraba hajoji ga kamfanin Apple, bisa fifikon da take da shi a fannin albarkatun kwararru da karsashin kirkire-kirkire.

Ya ce kamfanin Apple zai ci gaba da dora muhimmanci ga ci gaban sa a kasar Sin cikin tsawon lokaci, kana zai ci gaba da kara zuba jari a fannonin rarraba hajoji, da bincike da samar da ci gaba, da kuma fannin sayar da hajojin sa a kasar.  (Saminu Alhassan)