logo

HAUSA

Sin ta yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai jihar Moscow ta kasar Rasha

2024-03-23 18:31:12 CMG Hausa

Dangane da harin ta'addancin da aka kai wani zauren nuna wasannin kade-kade dake jihar Moscow ta kasar Rasha a jiya da dare, wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce, bangaren Sin ya kadu da jin aukuwar wannan mummunan harin ta'addanci, wanda ya haifar da mummunar asarar rayuka. Inda kasar Sin ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu, da fatan samun sauki da wadanda suka jikkata. Sin na adawa da duk wasu nau'ikan ayyukan ta'addanci, tana kuma Allah wadai da harin ta'addanci, kana tana goyon bayan kokarin gwamnatin kasar Rasha na wanzar da tsaron kasa da samar da daidaito. (Bello Wang)