logo

HAUSA

Shugaban Angola: Sin tana hadin gwiwa tare da kasashen Afirka maimakon mulkin mallaka

2024-03-23 16:11:45 CMG Hausa

Shugaban kasar Angola João Manuel Gonçalves Lourenço, ya ce al’ummun kasashen yamma sun yi mulkin mallaka a kasashen Afirka na tsawon wasu karnuka ciki har da kasar sa, amma ba su bar wasu abubuwan more rayuwa masu inganci a wuraren ba. Sai dai a halin yanzu, an kyautata samar da ababen more rayuwa sosai a kasashen Afirka, cikin shekaru kasa da 50, ta hanyar tallafi da Sin da sauran kasashen duniya suka bayar.

Shugaba Lourenco ya bayyana hakan ne kwanan baya, yayin wata zantawa da ya yi da dan jaridar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, lokacin da yake ziyarar aiki a kasar Sin. 

Game da kuskuren fassara rawar da kasar Sin take takawa a kasashen Afirka, da kafofin watsa labaran kasashen yamma suke yi, shugaban na Angola ya ce irin wadannan kafofi dake zargin kasar Sin daga kasashen yamma, a hakika suna yi wa kasar Sin batanci ne saboda mugunta. 

Ya ce ko shakka babu, kasar Sin tana hadin gwiwa tare da kasashen Afirka maimakon mulkin mallaka. Kaza lika al’ummun Sin suna zuwa yankunan Afirka tare da jari da fasahohi, wanda hakan ya kawo ci gaba ga kasashen nahiyar. 

A cikin shekaru 22 da suka gabata, an kawo karshen yaki a Angola, bayan da kasar ta zama kango baki daya. Amma yanzu haka, bisa tallafi, da goyon bayan Sin, an hade sassan kasar da hanyoyin mota, tsakanin larduna da birane, kuma an maido da hanyoyi, da gadoji, da tashoshin jiragen ruwa, da kuma hanyoyin jiragen kasa. 

Idan masu zargi na kasashen yamma, suna tsammanin za su iya yin abun da ya fi hakan, to kamata ya yi su nuna a aikace, a maimakon ci gaba da yi wa Sin batanci. (Safiyah Ma)