logo

HAUSA

Sin ta raba basira da karfinta na inganta warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa

2024-03-22 19:53:01 CMG Hausa

A yau Jumma’a ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Inda ya yi tsokaci game da wasu abubuwa da suka shafi ayyukan diplomasiyya karo na biyu, wadanda wakilin musamman dake kula da harkokin Turai da Asiya na Sin ya gudanar. Lin Jian ya bayyana cewa, wakilin musamman dake kula da harkokin Turai da Asiya na gwamnatin Sin Li Hui, ya tattauna da bangarori daban daban, kan yadda za a gaggauta tsagaita bude wuta, da kuma inganta warware rikicin siyasa da sauransu, yayin da ya ziyarci kasashen Rasha da Ukraine, da sauran wasu kasashen Turai da batun ya shafa.

Bangarori daban daban sun yaba wa bangaren Sin, bisa kokarinsa na gudanar da aikin shiga-tsakani, sun kuma yi imani cewa, a matsayin kasa mai kujerar dindindin a MDD kuma kawa ga Rasha da Ukraine, Sin za ta iya mika sakonni tsakanin kasashen biyu, har da sauran bangarori daban daban, ta yadda za a ingiza dukkan bangarorin su nemi matsaya guda, tare da kiyaye bambance-bambance tsakaninsu, da tattara muradu masu kyau don gudanar da tattaunawar zaman lafiya.

Game da ziyarar da firaministan Eswatini Russell Dlamini ya kai yankin Taiwan a kwanan nan, Lin Jian ya bayyana cewa, kasar Sin na matukar adawa da keta manufar kasar Sin daya tak da kuma ikon mallakar yankunan kasar.

Har ila yau, game da sanarwar da kungiyar EU ta fitar, a fannin yin rajistar kwastan kan motoci masu amfani da lantari da ake shigarwa Turai daga kasar Sin, wanda ake ganin mai yiwuwa a sanya musu "Harajin kwastan mai tsauri", da kuma batun da ake yi cewa kasashen Birtaniya da Amurka na shirin gudanar da bincike mai nasaba da tsaron kasa, kan ababen hawa masu aiki da lantarki da ake kerawa a kasar Sin, Lin Jian ya bayyana cewa, motocin dake amfani da wutar lantarki bangare ne na masana’antar kasa da kasa, kuma ba za a samu nasara ba har sai an yi hadin gwiwa, kana ba za a samu ci gaban fasahohi ba, har sai an gudanar da takara cikin adalci.

Ya kara da cewa, ba da kariya ga cinikayya ya karya ka’idar tattalin arzikin kasuwanni, da kuma kungiyar cinikayyar kasa da kasa. Kaza lika a nan gaba, wannan zai gurgunta moriyar masana’antu, da masu sayayyar kasa da kasa, kana zai yi mummunan tasiri ga sauyin tattalin arzikin duniya maras gurbata muhalli, da kuma kokari na tinkarar sauyin yanayi. (Safiyah Ma)