logo

HAUSA

Rikicin kabilanci ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 40 a Chadi

2024-03-22 16:17:05 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da tsaron al’umma da shige da fice ta kasar Chadi, ta ce mutane akalla 42 sun mutu biyo bayan rikicin kabilanci tsakanin wasu al’ummomi dake gabashin kasar.

Ma’aikatar ta ce rikicin ya kai ga kona wani kauye, kana an cafke mutane 175. Sai dai, ba ta bayyana ainihin musabbabin rikicin ba.

Kafafen yada labarai a kasar sun ruwaito cewa, rikicin ya auku ne ranar Laraba tsakanin al’ummomin Mouro da Birgut na lardin Quaddai dake gabashin kasar. (Fa’iza Mustapha)