logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da ka’idojin aiwatar da haramcin kamun kifi na tsawon shekaru 10 a kogin Yangtze

2024-03-22 10:40:10 CMG Hausa

Kasar Sin ta gabatar da ka’idojin dake dauke da kudurinta na aiwatar da haramcin aikin kamun kifi a kogin Yangtze na tsawon shekaru 10.

A cewar daftarin ka’idojin, wanda babban ofishin majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya fitar, haramcin kamun kifin wani muhimmin mataki ne na inganta ci gaba mai inganci a yankin zirin tattalin arziki na Yangtze da kuma farfado da kuzarin kogin da ake wa kirari da ‘uwa’ a kasar Sin.

A cewar ka’idojin, ya kamata sassan gwamnati masu ruwa da tsaki su dauki batun aiwatar da haramcin a matsayin aiki mafi muhimmanci. Haka kuma, su karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu da sa ido da daukaka hanyoyin aiwatar da doka da inganta hadin gwiwa tsakanin sassa da yankuna daban-daban wajen aiwatar da dokoki.

Bugu da kari, ka’idojin sun kuma bukaci a yi kokarin matse kaimi wajen kare halittun dake fuskantar bacewa da wadanda ba kasafai a kan same su ba, a fadin kogin. Haka zalika, sun bukaci a dauki matakan farfado da muhallan halittu da karfafa karewa da kula da halittun dake bakin wurare, da gaggauta farfado da muhallin halittu. (Fa’iza Mustapha)