logo

HAUSA

Yawan masu amfani da yanar gizo a Sin ya zarce biliyan 1

2024-03-22 16:34:10 CGTN HAUSA

Cibiyar sadarwar yanar gizo ta kasar Sin wato CNNIC ta gabatar da rahoton yanayin bunkasuwar yanar gizo a kasar Sin karo na 53 a yau Jumma’a a Beijing, inda ya nuna cewa, ya zuwa karshen watan Disamba na bara, yawan masu amfani da yanar gizo a kasar ya kai biliyan 1 da miliyan 92, adadin da ya karu da miliyan 24.8, idan aka kwantanta da na makamancin lokacin shekara na 2022. Ke nan ana nufin cewa, kaso 77.5 bisa dari na al’ummar kasar Sin na amfani da yanar gizo ta Intanet.

Ban da wannan kuma, alkaluman sun bayyana cewa, tattalin arzikin Sin ya ci gaba da samun ingantacciyar karuwa kuma mai dorewa, duba da rawar ganin da yanar gizo ke takawa a fannin ingiza sabbin masana’antu da bunkasa sabbin karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko da bunkasuwar tattalin arziki da al’umma. (Amina Xu)