logo

HAUSA

Sin na daukar matakan da suka kamata na shiga yarjejeniyar CPTPP

2024-03-21 20:05:50 CMG Hausa

Ma’aikatar cinikayya ta Sin, ta gudanar da taron manema labarai a Alhamis din nan, inda a yayin zaman kakakin ma’aikatar He Yadong, ya gabatar da ci gaban da aka samu, game da aniyar kasar Sin ta shiga cikakkiyar jarjejeniyar hadin gwiwar raya cinikayya tsakanin kasashen yankin tekun Fasifik ko CPTPP a takaice.

He Yadong, ya ce tun bayan gabatar da bukatar shiga yarjejeniyar, Sin ta zanta, da gudanar da shawarwari da dukkanin kasashe mambobin yarjejeniyar bisa tsare tsaren da aka tanada.

Kaza lika, Sin ta aiwatar da matakai na daidaita matsayinta ta yadda zai dace da matsayin inganci na kasa da kasa ta fuskar bin dokokin tattalin arziki da cinikayya, ta kuma yi namijin kokari, wajen aiwatar da sauye sauye, da gudanar da ayyukan gwaji a sassa masu alaka, kana ta cimma nasarori a fannin. A mataki na gaba kuma, Sin za ta ci gaba da ingiza matakan shiga yarjejeniyar ta CPTPP, bisa tsarin da aka tanada na yin hakan.

Game da tsarin cinikayyar sassan hada na’urorin laturoni na “semiconductor” kuwa, He Yadong ya ce a cikin tsawon lokaci, Amurka ta dunkule komai cikin batun tsaron kasa, ta karya ka’idojin fitar da hajoji, da sauran matakan gurgunta kasuwa, kana ta katse tsarin samar da “semiconductor” a kasuwannin duniya, matakin da ya yi matukar karya dokokin kasuwanci, da na tattalin arziki da cinikayya, matakin da ko shakka babu zai illata tsarin samar da “semiconductor” ga sassan dake bukata. (Saminu Alhassan)