logo

HAUSA

Babban jami’i a Habasha ya yi kira da a karfafa hadin gwiwa da Sin

2024-03-21 21:15:33 CMG Hausa

Babban darakta mai lura da harkokin Gabas ta tsakiya, da Asiya, da yankin Fasifik a ma’aikatar harkokin wajen kasar Habasha Gebeyehu Ganga, ya yi kira da a kara yaukaka hadin gwiwar dake tsakanin Habasha da Sin, karkashin dandaloli da ake da su, da ma sabbin shirye shirye.

Gebeyehu Ganga, ya yi kiran ne yayin wani taron karawa juna sani da aka shirya game da “shawarar ziri daya da hanya daya” ko BRI, a jiya Laraba a birnin Addis Ababan kasar Habasha.

Jami’in ya ce Habasha da Sin sun ci gajiya ta tsawon lokacin kawance, wanda ya haura shekaru 50, amma duk da haka, akwai bukatar kara inganta hadin gwiwa, da yaukaka abota tsakanin sassan 2. (Saminu Alhassan)