logo

HAUSA

Kwararrun Afirka sun nuna yabo ga dimokuradiyyar Sin

2024-03-21 14:18:14 CMG Hausa

A jiya Laraba ne, aka bude dandalin tattaunawa kan dimokuradiyya na kasa da kasa karo na uku mai taken “dimokuradiyya, darajar dan Adam ta bai daya” a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Shugaban cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta kasar Nijeriya Charles Onunniju ya halarci taron, kuma a yayin da yake zantawa da dan jaridar Babban Gidan Rediyo da Talabijin Na Kasar Sin wato CMG, ya bayyana cewa, irin dimokuradiyya ta kasar Sin ta kan daidaita da samun kyautatuwa bisa yanayi da halin da ake ciki, lamarin da ya tabbatar da gudanarwar harkokin da abin ya shafa yadda ya kamata, tare da samar da tallafin da al’ummar Sin ke bukata.

Haka kuma, ya nuna damuwa kan yanayin dimokuradiyya a yammacin kasashen duniya. Yana mai cewa, dimokuradiyyar yammacin kasashen duniya tana raguwa, bunkasuwar jam’iyyu masu tsattsauran ra’ayi ta yi nuni da wannan matsalar. Shi ya sa, ya yi kira ga kasashen duniya da su yi mu’amala bisa ka’idar girmama juna, domin neman bunkasuwar duniyarmu cikin lumana.

Dangane da tsarin dimokuradiyyar da ya shafi al’umma baki daya, darektan zartaswar na cibiyar nazarin kasar Sin da kasashen Afirka ta kwalejin nazarin manufofin nahiyar Afirka na kasar Kenya, Dennis Munene Mwaniki ya bayyana cewa, akwai muhimman batutuwa guda uku dake goyon baya wannan tsari, su ne, bautawa al’umma, da jagorancin Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, da kuma bin dokokin kasa. Ya kuma kara da cewa, irin wannan tsari zai ba da taimako ga wasu kasashen Afirka wajen fitar da su daga mawuyacin hali. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)