logo

HAUSA

Xi Jinping ya nanata wajibcin yin kwaskwarima da kirkire-kirkire cikin hakikanin hali a lardin Hunan

2024-03-21 16:38:51 CGTN HAUSA

Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar JKS kana shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin koli na sojan kasar, Xi Jinping ya nanata a rangadin da ya yi a lardin Hunan cewa, dole ne Hunan ya nace ga matsayinsa a cikin tsare-tsaren samun sabon ci gaba da aka tsayar, kuma ya nace ga samun bunkasuwa mai karko da inganci, kana da yin kwaskwarima da kirkire-kirkire da rikon gaskiya. Ban da wannan kuma, Hunan ya gaggauta bunkasa bangaren masana’antun samar da kayayyaki, da kuma bangaren kirkire-kirkire bisa kimiyya da fasaha.

A yau da safe, Xi Jinping ya saurari rahoton aikin gwamnatin lardin Hunan, inda ya bayyana gamsuwarsa game da ci gaban da lardi ke samu a mabambanta bangarori.

A cewarsa, kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha abu ne mafi muhimmanci wajen bunkasa sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko. Ya kamata a kara kokarin yin kirkire-kirkire a mabambanta sana’o’i bisa kirkire-kirkire a fannin kimiya da fasaha. Ban da wannan kuma, ya kamata lardin ya yi musanyar ra’ayi da hukumomin kimiyya na kasar, da ma shigar da hukumomi masu fifiko a bangaren nazari daga kasashen waje, ta yadda zai kai ga daga karfin yin kirkire-kirkire a wasu muhimman fannoni. (Amina Xu)