logo

HAUSA

Xi ya aika sakon taya murna ga Prabowo Subianto da ya lashe babban zaben kasar Indonesiya

2024-03-21 11:40:52 CMG Hausa

Jiya Laraba, shugaban kasar Sin ya kira mista  Prabowo Subianto, domin taya shi murnar lashe babban zaben kasar Indonesiya.

Xi Jinping ya ce, kasar Sin da kasar Indonesiya suna da zumuncin gargajiya, kana, bisa kokarin da bangarorin biyu suka bayar, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na bunkasuwa da sauri, ana kuma ci gaba da zurfafa fahimtar juna kan harkokin siyasa a tsakanin kasashen biyu, da karfafa yin mu’amalar manyan tsare-tsaren neman bunkasuwa, inda suka cimma sakamako da dama bisa hadin gwiwarsu, yayin da suka bude sabon babin karfafa dunkulewar kasashen biyu.

Ya kuma kara da cewa, kasar Sin tana mai da matukar hankali wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ya yi fatan yin hadin gwiwa da shugaba Prabowo Subianto, domin cimma sakamako mai gamsarwa a fannin karfafa dunkulewar kasashen biyu, da kuma kafa abin koyi a fannin habaka hadin gwiwar dake tsakanin manyan kasashe masu tasowa domin neman ci gaba tare, ta yadda za a kara tallafa wa al’ummomin kasashen biyu, tare da samar da babban karfi ga bunkasuwar yankin baki daya, har ma da dukkanin kasashen duniya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)