logo

HAUSA

An fara taron kasa da kasa kan tsarin dimokuradiyya karo na uku a nan birnin Beijing

2024-03-20 15:43:24 CMG Hausa

A yau Laraba ne aka bude dandalin tattaunawa kan dimokuradiyya na kasa da kasa karo na uku mai taken darajar dan Adam ta bai daya, a nan birnin Beijing.

Kusan jami'ai da masana 300 daga kasashe da yankuna 70 sun tattauna yadda za a tabbatar da dimokuradiyya a wannan zamani na dijital.

An gabatar da jawabai don zaburar da tattaunawa a kananan matakai na taron, da nazarin fannoni hudu na dimokuradiyya, da suka hada da tsarin zamanintar da mulki na zamani, gudanar da Mulki bisa doka a wannan zamani na dijital, sabon tsarin mulkin duniya na gaba bisa fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, da kuma tsarin mulki na gama gari a cikin duniya mai mabambantan tsarin mulki. (Mohammed Yahaya)