logo

HAUSA

Sin Ta Nuna Fasahohin Zamani A Taron Baje Kolin Masana’antun Nukiliya Na Duniya

2024-03-20 12:07:21 CMG Hausa

Jiya Talata 19 ga wata ne aka bude taron baje kolin masana’antun nukiliya na kasa da kasa karo na 17 a nan Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda kamfanoni fiye da 100 na gida da wajen kasar Sin suka halarta, wadanda suka nuna sabbin fasahohi, injuna da hanyoyin yin amfani da su a fannin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin nukiliya.

A matsayinsa na daya daga cikin tarukan baje kolin masana’antun nukiliya mafiya tasiri a duniya, taron baje kolin din da ake gudanarwa a Beijing ya kasance dandalin gwada fasahohi da hajoji da manyan injuna masu nasaba da masana’antun nukiliyar kasar Sin.

A yayin taron na bana, kamfanin masana’antun nukiliyar kasar Sin CNNC ya sanar da cewa, karo na farko ne zai bude kofar gine-ginen nazarin masana’antun nukiliya da dandalin gwaje-gwaje guda 10 ga kasashen duniya, wadanda suka hada da ginin Huanliu-3 na gwajin fasahar sarrafa birbishin nukiliya da ake amfani da shi a fasahar samar da sabon nau’in rana ta bil Adama, da kuma dakin gwaje-gwajen Beishan da ke karkashin kasa har mita 560.(Tasallah Yuan)