logo

HAUSA

Sin Ta Harba Tauraron Dan Adam Na Queqiao-2

2024-03-20 12:04:19 CMG Hausa

A safiyar yau Laraba da karfe 8 da mintoci 31 ne aka samu nasarar harba tauraron dan Adam mai karbar umarni daga kasa, samfurin Queqiao-2, da rokar Long March-8 Y3, zuwa sararin samaniya, daga cibiyar harba kumbuna ta Wenchang, dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin.

A cewar hukumar lura da sararin samaniyar kasar Sin ko CNSA, tauraron dan Adam na Queqiao-2 zai taka muhimmiyar rawa a mataki na 4 na shirin binciken duniyar wata na Sin, wanda zai karbi umarni daga doron kasa da kuma ba da hidimomin sadarwa ga na’urorin binciken duniyar wata na Chang’e masu lamba 4 da 6. (Tasallah Yuan)