logo

HAUSA

Xi ya jaddada ba da jagoranci ga dalibai don yi wa kasa hidima a matsayin manufar gudanar da makarantu

2024-03-20 14:59:25 CMG Hausa

Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada cewa, manufar gudanar da makaranta, ba wai don daukaka darajar dalibai kawai ba, har ma da yi musu jagora wajen yi wa kasa hidima.

Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci daya daga cikin harabar jami’ar farko ta Hunan a ranar Litinin din da ta gabata yayin wani rangadi da ya kai birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin.

Kazalika, yayin rangadinsa a wani kauye a birnin Changde da ke lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin a ranar Talata, Xi ya saurari rahoto daga jami'an kauyen kan kokarin da yankunan ke yi na saukaka wa masu aiki a matakin farko dawainiyar aiki a yankunan karkara a ’yan shekarun nan. (Mohammed Yahaya)