logo

HAUSA

Sin na shirin kaddamar da gangamin bunkasa samar da guraben ayyukan yi ga daliban da suka kammala jami’o’i

2024-03-20 20:00:52 CMG Hausa

Ma’aikatar ilimi ta kasar Sin MOE, ta ce za ta kaddamar da gangamin bunkasa samar da guraben ayyukan yi ga daliban da suka kammala karatu a jami’o’i, yayin zangon karatu na bazara, muhimmin lokaci na daukar aiki a makarantun.

Ma’aikatar ta MOE, na fatan amfani da wannan dama wajen hallara sama da sassan sana’o’i 10,000, domin su dauki dalibai aiki a kamfanoninsu, a hannu guda shirin zai karfafa gwiwar jami’o’i, su rika ziyartar kamfanoni, su jawo bayanan samar da guraben aiki, da ankarar da dalibai da suka kammala karatu damammakin da suka dace da su.

Har ila yau, ana bukatar jami’o’i su yiwa dalibai masu neman aiki jagora, ta hanyoyi daban daban na samar da bayanai, kamar jawabai ta yanar gizo da sauran su. (Saminu Alhassan)