logo

HAUSA

Kamfanin kasar Sin zai gina filin wasan kwallon kafa na zamani a arewacin Tanzaniya domin buga gasar AFCON na shekarar 2027

2024-03-20 10:56:59 CMG Hausa

Kamfanin shimfida layin dogo na kasar Sin (CRCEG) a ranar Talata ya ratttaba hannu kan wata yarjejeniya da ma’aikatar al’adu da fasaha da wasanni ta kasar Tanzaniya kan gina filin wasan kwallon kafa a birnin Arusha da ke arewacin kasar Tanzaniya domin gasar cin kofin Afirka na shekarar 2027 (AFCON).

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce filin wasa mai kujeru 30,000 da za a gina a kan kadada 14.57, zai cika ka'idojin hukumar kwallon kafa ta Afirka da kuma hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.

Tanzania za ta karbi bakuncin gasar AFCON ta 2027 tare da Kenya da Uganda. (Mohammed Yahaya)