logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da tsarin amfani da kudin Yuan ta wayar salula domin saukakawa baki

2024-03-19 10:55:51 CMG Hausa

Babban bankin kasar Sin, ya fitar da wani tsarin amfani da kudin Yuan ta na’ura wato e-CNY, a yunkurinsa na baya-bayan nan, na saukaka biyan kudi ta wayar salula ga baki.

A cewar babban bankin, masu amfani da wayar salula na iya neman manhajar “e-CNY” a kasuwar manhajoji ta App Store ko Google Play, domin sauke manhajar da kuma sanya tsarin amfani da yuan ta naura, sannan su yi regista domin samun asusu. Daga nan sai a danna inda aka rubuta "Open/Add e-CNY Wallets" wato bude jakar kudi ta wallet, sai a zabi hanyoyin biyan kudin da aka sahalewa bayar da hidimomi ga baki domin kammala registar, kana a fara amfani da jakar kudi ta e-CNY Wallet. 

Sanarwar da bankin ya fitar a jiya, ta ce za kuma a iya yin registar jakar kudi ta e-CNY Wallet ne ta hanyar amfani da lambobin waya na kasashe da yankuna sama da 210.

A farkon watan nan ne kuma tsare-tsaren biyan kudi ta wayar salula na manyan manhajojin biyan kudi na kasar Sin wato Alipay da WeChat suka sanar da cewa, a yanzu baki za su iya hada katunan karbar rance na bankunan kasashen waje, wato Credit Card da manhajojin, kuma katunan sun hada irin na Visa da Master. (Fa’iza Mustapha)