logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya yi rangadi a Changde na lardin Hunan

2024-03-19 19:15:13 CMG Hausa

A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a birnin Changde na lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin.

Yayin rangadin nasa, Xi ya ziyarci titin raya al’adu, da kuma wani kauye dake birnin. Ya kuma ganewa idanun sa yadda aka farfado da gajiyar yankunan tarihi da al’adu, da yadda aka kyautata lura da muhallin ruwan birnin, da shirin aikin noman bazara, da kyautata tsarin jagorancin al’umma a matakin farko.

A lokacin da yake ganewa idon sa filin noman shinkafa dake wurin, ya ce kyautata aikin gyaran filin noma gabanin shuka, na da matukar muhimmanci ga samar da yabanya mai yalwa, da isasshen abinci.

Shugaban na Sin ya kara da cewa, ya wajaba ko wane yanki da sashe ya tabbatar da nasarar manoma, ta samun isasshen kudin shiga daga hatsi, a kuma ingiza sha’awar manoma ta rungumar noman hatsi, tare da samar da kyakkyawan mafari na fadada yawan hatsin da ake nomawa, da kudin shigar manoma a duk tsawon shekara.  (Saminu Alhassan)