logo

HAUSA

Sin ta fitar da tsarin ingiza bude kofa a matsayin koli da jawo jarin waje

2024-03-19 21:22:57 CMG Hausa

Babban ofishin majalissar zartaswar kasar Sin, ya fitar da tsarin cimma nasarar ingiza bude kofa bisa matsayin koli, bisa daidaito da yin aiki tukuru, don jawowa, da cin gajiyar jarin waje.

Tsarin ya tanadi aiwatar da matakai 24 a bangarori 5, ciki har da fadada damar shiga kasuwanni, da inganta kira ga masu zuba jari daga waje, da samar da damar bai daya ta raya cinikayya, da ingiza shigowar ginshikan kirkire-kirkire, da kuma daidaita tafiya tsakanin dokokin cikin gida da na raya tattalin arziki da cinikayyar kasa da kasa masu inganci. (Saminu Alhassan)