logo

HAUSA

Sin ta fitar da ka’idoji game da aiwatar da dokar kare hakkokin masu sayayya

2024-03-19 20:22:35 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya sanya hannu kan dokar majalissar zartaswa, mai kunshe da ingantattun ka’idojin aiwatar da dokokin kasa, na kare hakkoki da moriyar masu sayayya.

Tun daga 1 ga watan Yulin shekarar nan ta 2024, dokar ta tanadi cikakkun tsare tsare, game da nauyin dake wuyan masu gudanar da kasuwanci, ciki har da kare hakkin masu sayayya da kadarorin su, da yadda za a warware matsalar kayayyakin da suka zo da nakasu, da kaucewa tallace-tallace masu cike da yaudara, da fayyace farashi, da tabbatar da ingancin hajoji, da kare bayanan masu sayayya.   (Saminu Alhassan)