logo

HAUSA

Sin: Abin da ya kamata a gaggauta yi a halin yanzu shi ne tsagaita bude wuta a zirin Gaza

2024-03-19 19:25:01 CMG Hausa

A yau Talata, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda a gun taron wani dan jarida ya yi tambayar da ta shafi rikicin Falasdinu da Isra’ila, da hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai asibiti mafi girma dake zirin Gaza. 

Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya bayyana cewa, rikicin Falasdinu da Isra’ila ya haura watanni 5, kana yanayin jin kai a wurin yana da matukar hadari, don haka abin da ya dace a gaggauta yi a halin yanzu, shi ne tsagaita wuta tsakanin Falasdinu da Isra’ila nan take, da yin iyakacin kokarin kiyaye tsaron fararen hula, da guje wa karin asarar rayuka, da kuma rage matsalolin jin kai. 

Ya kara da cewa, bangaren Sin yana so ya ba da gudummawarsa, wajen kyautata yanayi mai hadari da ake fuskanta a halin yanzu, da kuma warware matsalar Falasdinu ta komawa hanyoyi na dadaito, na manufofin kasashen biyu, a hadin gwiwarsa tare da bangarori daban daban.

Game da batun Ukraine, Lin Jian ya bayyana cewa, a ko da yaushe bangaren Sin yana tsaya wa tsayin daka kan matsayar adalci, da dagewa wajen gudanar da tattaunawa don samun zaman lafiya. Bangaren Sin yana goyon bayan gudanar da taron tattaunawa na kasa da kasa, wanda bangarorin Rasha da Ukraine suka amince, inda za a tattauna dukkan manufofin zaman lafiya cikin adalci.

Game da alkawarin tabbatar da tsaro da Amurka ta yi wa Philippines kuwa, Lin ya bayyana cewa, Amurka ba bangare ne da ya shafi batun tekun kudancin kasar Sin ba, don haka kasar ba ta da ikon tsoma baki cikin batun da ya shafi tekun, tsakanin Sin da Philippines. Ya ce hadin gwiwar Amurka da Philippines bai kamata ya gurgunta ikon mulkin kai, da moriyar teku da Sin take da su a tekun kudancin kasar ba. A sa’i daya kuma, bai kamata ta nuna goyon baya ga ayyukan karya dokoki da Philippines ta aiwatar ba. (Safiyah Ma)