logo

HAUSA

Xi ya yi rangadi a birnin Changsha na lardin Hunan da ke tsakiyar kasar Sin

2024-03-19 11:19:42 CMG Hausa

Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a birnin Changsha na lardin Hunan da ke tsakiyar kasar Sin a jiya Litinin.

Ya ziyarci harabar jami’ar horar da malamai ta farko ta Hunan da ke Chengnan da kamfanin batir na BASF Shanshan. Ya fahimci irin kokarin da jami'ar ke yi na kyautata yin amfani da albarkatun da suka shafi al'adun Jam'iyyar, da kiyaye nagartattun dabi’u ta hanyar ilimi, da yunkurin cikin gida na hanzarta raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, da kuma fadada babban matakin bude kofa ga kasashen duniya. (Yahaya)