logo

HAUSA

MTC da Huawei sun gudanar da gwajin 5G na farko a hukumance a Namibia

2024-03-19 09:57:04 CMG Hausa

A jiya Litinin ne kamfanin sadarwa mafi girma na kasar Namibia MTC da kamfanin fasahar sadarwa na kasar Sin Huawei suka gudanar da gwajin farko na fasahar 5G a birnin Windhoek, babban birnin kasar.

Wannan gwajin ya zo ne bayan da gwamnati ta dage dakatar da 5G kuma hukumar kula da sadarwa ta Namibia ta ware aikin samar da fasahar 5G ga MTC da sauran kamfanonin sadarwa a kasar.

Ministar yada labarai, sadarwa da fasaha ta Namibia Emma Theofelus ta bayyana taron a matsayin wani muhimmin ci gaba ga Namibia, inda ta jaddada muhimmancin amfani da sabbin fasahohin zamani don ciyar da kasa gaba.

Huawei ya yi aiki tare da MTC tsawon shekaru don kawo fasahar 3G, 4G, da 4.5G zuwa Namibiya. (Yahaya)