logo

HAUSA

An yi bikin mu’amalar matasa da yaran Sin da Amurka a birnin Beijing

2024-03-19 10:46:50 CGTN HAUSA

 

Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da kungiyar raya mu’amalar daliban Amurka da Sin sun kaddamar da bikin mu’amalar matasa da yaran Sin da Amurka mai taken “Zuwan abokai daga nesa”, a jiya Litinin a nan birnin Beijing, wanda ya kasance wani bangare na mu’amala tsakanin matasan Amurka dubu 50 wadanda ke ziyara a Sin, da kuma takwarorinsu na kasar Sin.

Shugaban CMG Shen Haixiong, da magajin birnin Strakon Richard Muri da mataimakin sakataren kungiyar raya mu’ammala kan aikin ba da ilmi na kasar Sin Fu Bo, sun halarci bikin tare da ba da jawabi, haka kuma abokai daga Sin da Amurka fiye da dari sun halarci biki.

Shen Haixiong ya ce, a bana ake cika shekaru 45 ta kafuwar huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Sin da Amurka. Kuma a watan Fabrairun bana, Xi Jinping da uwar gidansa Peng Liyuan, sun mikawa dalibai da malaman makarantar midil na Lincoln ta Amurka katin murnar sabuwar shekara tare da yi musu fatan alheri, da gayyatarsu zuwa nan kasar Sin, domin sun yi imanin cewa, za su fahimci ainihin kasar Sin ta hanyar gani da idanunsu da saurara da kunnuwansu da kuma dandana da bakinsu. (Amina Xu)