logo

HAUSA

Dalilin Farfadowar Tattalin Arzikin Sin

2024-03-19 10:53:02 CGTN HAUSA

Kwanan baya, babban darektan kamfanin Plymouth Rock James Stone ya shaidawa manema labarai na CMG cewa, “Na yi imani da cewa, sha’anin ba da jiyya zai bunkasa cikin sauri a shekaru 5 zuwa 10 masu zuwa a kasar Sin.” Ban da wannan kuma, a cewar sauran kamfanonin ketare, ba za a iya maye gurbin kasuwar kasar Sin ba, duba da makoma mai haske da ci gaban tattalin arzikin kasar ke da ita.

To, mene ne dalilin da ya sa haka? Bari mu duba yadda tattalin arzikin Sin ya gudana a watanni 2 na farkon bana. Yawan darajar kayayyakin da manyan masana’antu suka samar ya karu da kashi 7% bisa makamancin lokaci na bara, 39 daga cikin manyan nau’o’in masana’antu 41 sun samu karuwa bisa bara, wato yawan nau’o’in masana’antun da suka samu karuwa ya kai kashi 95.1%. Wadannan alkaluma na bayyana cewa, makoma mai haske na karuwar tattalin arzikin Sin cikin dogon lokaci bai canja ba. Kuma an samu mafari mai kyau da ci gaba da farfadowa cikin tsanaki a wannan shekara.

Idan aka duba kasuwar tattalin arzikin Sin, za a iya ganin bunkasuwa a ko ina. Alal misali, a watan Janairu da Faburairu, yawan kudaden da aka kashe kan kayayyakin masarufi ya karu da kashi 5.5% bisa na makamancin lokacin bara, abin da ya bayyana karin karfin sayayya. Baya ga haka, ba za a raba kirkire-kirkire da batun ci gaban tattalin arziki ba, kazalika, yawan na’urorin buga kayayyaki irin na 3D da na’urorin caji na samar da wutar lantarki ga motoci da sassan kayayyakin lantarki da aka samar ya karu da kashi 40% bisa makamancin lokacin bara, kuma yawan jarin da aka zubawa sana’ar kimiya da fasaha ta zamani ya karu da kashi 9.4% bisa makamancin lokacin bara. Hakan ya bayyana kuzarin da kwaskwarima ta haifar, kan karfin samar da kayayyaki.

Mabambanta kamfanonin ketare masu tarin yawa sun zo nan kasar Sin duba da halayya mai yakini ta kirkire-kikire ta kasar. A watan Janairu, adadin sabbin kamfanonin ketare da aka kafa a kasar ya kai 4588, wanda ya karu da kashi 74.4%, inda yawan kudaden da kasashen yamma ke zubawa Sin ya rika karuwa.

Ba shakka, Sin za ta cimma muradunta na raya tattalin arziki a bana, ganin yadda ake samun bunkasuwa a bangarori daban-daban da kuzarin kasuwa da kwarin gwiwar kamfanoni. (Amina Xu)