logo

HAUSA

Tattalin arzikin Sin ya bunkasa cikin tsanaki a watan Janairu da Fabrairu

2024-03-18 14:29:16 CGTN HAUSA

 

Hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar da alkaluma na watanni 2n farko na shekarar bana, alkaluman da suka nuna cewa, bukatar kayayyakin ta gudana bisa daidaito, da 'yar karuwa kadan, kuma bangaren samar da ayyukan yi, da farashin kayayyaki na gudana yadda ya kamata, lamarin da ya yi nuni ga ingantuwar ci gaban kasar, da ma mafari mai kyau, da makoma mai haske ta farfadowar tattalin arzikin kasar a nan gaba.

Ban da wannan, alkaluman sun kuma nuna cewa, ana samun bunkasuwar harkokin shige da fice cikin sauri, duba da yadda tsarin cinikin kasuwanni ke ci gaba da kyautatuwa. Daga watan Janairu zuwa Fabrairu, darajar yawan hajojin da Sin ta yi shige da ficen su ta kai RMB Yuan fiye da triliyan 6, kwatankwacin fiye da dala biliyan 918, adadin da ya karu da kashi 8.7% bisa na makamancin lokaci a bara.

A bangaren samar da aikin yi kuwa, shi ma yana gudana cikin daidaito, inda yawan kudaden da fararen hula suka rage kashewa ya dakata, inda raguwarsa ya karkata zuwa karuwa. A cikin watannin 2, matsakaicin yawan rashin aikin yi a garuruwa da birane ya tsaya kan kaso 5.3%, inda ma’aunin CPI ya yi daidai da na makamancin lokaci a bara, wato adadin ya ragu da kashi 0.8% a watan Jarairu, da kuma karu da kashi 0.7% a watan Fabrairu. (Amina Xu)