logo

HAUSA

Majalisar gudanarwar kasar Libya ta jaddada goyon bayanta ga MDD domin tabbatar da an gudanar da zabe

2024-03-18 13:56:59 CMG Hausa

Mataimakin shugaban majalisar gudanarwar kasar Libya Abdallah Al-Lafi a ranar Lahadi ya jaddada goyon bayan majalisar ga kokarin da tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta UNSMIL ke yi na ganin cewa an gudanar da babban zabe a kasar.

Al-Lafi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da Abdoulaye Bathily, wakilin musamman na babban sakataren MDD a kasar Libya kuma shugaban hukumar UNSMIL a Tripoli, babban birnin kasar, a cewar wata sanarwa da majalisar ta fitar.

A nasa bangaren, Bathily ya jaddada goyon bayansa ga majalisar gudanarwar kasar domin cimma sulhu a kasar, a cewar sanarwar.

Libya ta gaza gudanar da babban zabe a watan Disamba na 2021 kamar yadda aka tsara a baya, saboda rashin jituwa tsakanin jam’iyyun kasar kan dokokin zabe. (Yahaya)