logo

HAUSA

Sin ta shirya harba tauraron dan Adam na Queqiao-2

2024-03-17 16:26:30 CMG Hausa

A jiya Asabar ne aka tsayar da tauraron dan Adam mai karbar umarni daga kasa, samfurin Queqiao-2, da rokar Long March-8 Y3, a cibiyar harba kumbuna ta Wenchang, dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin, a wani bangare na shirin harba su zuwa samaniya.

A cewar hukumar lura da sararin samaniyar Sin ko CNSA, nan gaba cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, a lokaci mafi dacewa za a harba sabon tauraron.

Queqiao-2, ko Magpie Bridge-2, zai rika ba da hidimomi ga zango na 4, na shirin binciken duniyar wata na Sin, da hidimomin sadarwa ga na’urorin binciken Chang'e lamba 4, da 6, da 7, da Chang'e-8.  (Saminu Alhassan)