logo

HAUSA

Rukunin farko na masu yawon bude ido da suka samu bizar tashar shige da fice ya isa Xinjiang

2024-03-17 15:21:42 CMG Hausa

A shekarar nan ta bana, rukunin farko na masu yawon bude ido ‘yan kasashen waje da suka samu bizar tashoshin shige da fice na kasar Sin sun isa jihar Xinjiang mai cin gashin kai dake arewa maso yammacin kasar Sin. Rukunin ‘yan yawon bude idon mai kunshe da mutane 6 daga kasar Uzbekistan, ya isa birnin Urumqi fadar mulkin jihar ta tashar binciken shige da fice da daren ranar Juma’a.

A farkon shekarar nan da muke ciki, hukumar shige da fice ta Sin NIA, ta gabatar da wasu jerin matakai na saukaka damar da baki ‘yan kasashen waje ke samu, ta shiga kasar Sin domin kasuwanci, neman ilimi da yawon bude ido.

A cewar ofishin biza dake filin jiragen saman birnin Urumqi, a bana an tsara samar da biza ga baki ‘yan kasashen waje, wadanda za su rika shiga kasar ta tashoshin shige da fice, da nufin biyan bukatun baki ‘yan kasuwa dake son ziyartar Xinjiang, tare da samar da karin hidimomi masu sauki da dacewa da bukatun su.  (Saminu Alhassan)