logo

HAUSA

Yadda dimokaradiyya ke aiki a kasar Sin

2024-03-17 16:01:05 CMG Hausa

Wang Yongcheng, mai larurar gani ne da ya rasa idanun sa sakamakon wani hadari da ya gamu da shi tun yana karami. A shekarar 2023 ne kuma an zabe shi a matsayin wakili a majalissar wakilan al’ummar kasar Sin wato NPC, wadda ita ce majalissar dokoki mafi girma a kasar Sin, inda ya zama Basine na farko, kuma mai larurar gani daya tilo dake cikin majalissar ta NPC. 

A matsayin sa na wakili mai larurar gani, yayin manyan tarukan NPC da CPPCC na Sin na shekarar bara, Wang ya gabatar da shawarar buga tarin litattafai domin dalibai masu larurar gani, shawarar da sassa masu ruwa da tsaki suka dora matukar muhimmanci kan ta.

A dai shekarar ta bara, kwamitin kundin mulki da doka na majalissar NPC, ya sanya shawarar Wang cikin jerin batutuwan da ya nazarta game da daftarin dokar samar kyakkyawan yanayin bai daya tare da masu bukata ta musamman. Daga bisani an shigar da shawarwarin Wang cikin dokar kasa, wadda aka fara aiki da ita tun daga watan Satumban shekarar ta 2023.

A yayin tarukan bana kuwa, Wang ya karbi kundin rahoton ayyukan gwamnati da aka samar da rubutun masu larurar gani. Ya kuma ce "Wannan ce dimokaradiyyar da maras gani kan iya tabawa”.

Kasar Sin na aiwatar da dabaru daban daban, na inganta tsarin majalissar wakilan jama’a, kuma sannu a hankali tana gina wani tsari cikakke na shigar da dimokaradiyyar al’umma cikin harkar mulki, don tabbatar da an dama da kowa a harkokin siyasa.

Ga misali, a shekarun baya bayan nan, Sin ta fara samar da cibiyoyin kananan wakilai a yankuna masu yawan al’umma, ta yadda jama’a za su iya gabatar da matsalolin su ga jami’an, ko su kira jami’i ta layukan sadarwa da aka tanada, ta yadda za su iya tattaunawa da su, su kuma taimaka musu wajen warware matsalolin su.   (Saminu Alhassan)