logo

HAUSA

CMG Ya Kaddamar Da Wani Shirin Yayata Labaran Kasar Sin Da Al’ummun Kasa Da Kasa Za Su Iya Shiga

2024-03-16 16:37:18 CMG Hausa

Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya kaddamar da wani shiri a jiya Jumma’a, wanda yake gayyatar jama’ar kasa da kasa su yayata labarai game da kasar Sin.

Shirin mai taken “Written in the Sky: My China Story” na bukatar daidaikun mutane a fadin duniya daga mabambantan wurare da suka taba zuwa kasar Sin, su bayar da labarai masu ban sha’awa da armashi game da zamansu a kasar. An kaddamar da shirin ne domin murnar cikar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin shekaru 75 da kafuwa.

Ana ba masu son shiga shirin kwarin gwiwar rubuta labaransu ta salo daban daban, kamar rubutun sharhi ko hotuna ko gajerun bidiyo ko kuma pastoci. Wadanda aka zaba daga ciki, za su samu damar nunawa a shirin talibijin na CMG. Shirin na da nufin yayata ra’ayoyin al’ummar duniya game kyakkyawar alakar dake tsakanin daidaikun mutane da kasar Sin.

Kafar karbar labarai za ta kasance a bude har zuwa ranar 31 ga watan Augusta, inda masu sha’awar shiga za su tura sakonninsu zuwa adireshin email na cctv4zgylc@163.com. (Fa’iza Mustapha)