logo

HAUSA

Shugaban Jamhuriyar Congo: Ra’ayin sabon mulkin mallaka ba shi da tushe

2024-03-16 16:26:05 CMG Hausa

Yayin da aka cika shekaru 60 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin kasar Sin da Jamhuriyar Congo, shugaban kasar Jamhuriyar Congo Denis Sassou-Nguesso ya tattauna da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG a birnin Brazzaville, inda ya bayyana cewa, cikin shekaru 60 da suka gabata ya ziyarci kasar Sin har sau 16, inda ya ga gagarumin canji da kasar Sin ta samu, yana mai jinjinawa ci gaban kasar. Kana ya yabawa hadin gwiwar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin kan ayyukan more rayuwa bisa yadda suka samar da moriya ga jama’ar kasarsa, yana mai bayyana raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya a matsayin wadda za ta samar da damarmakin ci gaba ga nahiyar Afirka.

Game da ra’ayin sabon mulkin mallaka da kasashen yammacin duniya suke yadawa, shugaba Sassou ya yi nuni da cewa, idan aka ambaci ra’ayin sabon mulkin mallaka, to dole ne a ambato ra’ayin tsohon mulkin mallaka. Ya ce kasar Sin ba ta mulkin mallaka a nahiyar Afirka, kuma babu alaka tsakanin Sin da ra’ayin sabon mulkin mallaka. Ya kara da cewa, wadanda ke yayata wannan ra’ayi, su ne suka taba yin mulkin mallaka a zamanin da, da yada ra’ayin sabon mulkin mallaka a yanzu da kuma nuna goyon baya ga ra’ayin nuna wariyar launin fata a nahiyar Afirka. (Zainab Zhang)