logo

HAUSA

Wang Yi ya taya Ishaq Dar murnar zama sabon ministan harkokin wajen kasar Pakistan

2024-03-16 20:08:28 CMG Hausa

Memban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya mika sako ga Ishaq Dar don taya shi murnar zama sabon ministan harkokin wajen kasar Pakistan.

Wang Yi ya bayyana cewa, Sin da Pakistan abokai ne kuma makwabta. A cikin shekaru 73 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakaninsu, kasashen biyu sun yi imani tare da goyon bayan juna da kuma tinkarar kalubale tare, don haka suna da aminci mai karfi kuma na musamman. Ya ce a cikin shekarun baya-bayan nan, shugabannin kasashen biyu sun yi mu’amala sau da yawa, da fadada hadin gwiwarsu, da raya hanyar hadin gwiwar tattalin arziki a tsakaninsu, da kuma zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a ko da yaushe. Har ila yau, ya ce Sin tana daukar huldar diplomasiyya a tsakaninta da Pakistan a matsayin mai muhimmanci, kana tana son yin kokari tare da kasar Pakistan wajen aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito kansu, da gaggauta raya makomar bai daya ta Sin da Pakistan a sabon zamani. (Zainab Zhang)