logo

HAUSA

Nazarin CGTN: Salon Demokuradiyyar Amurka Na Da Tawaya

2024-03-16 20:01:12 CMG Hausa

Duk da cewa ta dade tana bayyana kanta a matsayin mafi hazikanci idan ana batun demokuradiyya, nazarin da kafar yada labarai ta CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da jami’ar Renmin ta kasar Sin suka gudanar ta hannun cibiyar bincike ta New Era International Communication, ya nuna cewa, kaso 71.1 na wadanda suka bayar da amsa yayin nazarin sun yi imanin cewa, tsarin siyasar Amurka ya yi hannun riga da aihinin manufar demokuradiyya. Wasu kaso 70.4 kuma ba su yarda cewa Amurka abun koyi ne a bangaren demokuradiyya ba, maimakon haka, suna ganin salon demokuradiyyar kasar na da tawaya.

Har ila yau cikin nazarin, wasu kaso 72.5 na ganin cewa, ana tunawa ne da batun muradun jama’a yayin zabe kadai, inda ‘yan siyasa kan manta da shi bayan zabe. Haka zalika, kaso 74.5 na mutanen da suka shiga nazarin na ganin cewa, salon demokuradiyyar Amurka na bayar da fifiko ga mutane kalilan masu wadata maimakon daukacin al’umma.

Jimilar mutane 39,315 daga kasashe 32 na fadin duniya ne suka bayar da amsa yayin nazarin jin ra’ayoyin jama’ar duniya guda 3, ciki har da nazari mai taken “Ra’ayoyi kan Amurka”. Kuma mutanen sun fito ne daga kasashe masu tasowa da suka hada da Afrika ta Kudu da Nijeriya da Brazil da India da Indonesia da Argentina. (Fa’iza Mustapha)