logo

HAUSA

Rundunar sojin Najeriya ta nemi taimakon kasashen duniya a kokarin da take yi na ceton daliban da aka sace a Kaduna

2024-03-16 15:48:42 CMG Hausa

Rundunar sojin Najeriya tana neman agajin kasashen duniya a aikin da take yi wajen ceto daliban da ‘yan bindiga suka sace a Kaduna da sauran mutanen da aka sace a sassan kasar daban daban.

Daraktan harkokin yada labarai na hedkwatar tsaron kasar Major Janaral Edward Buba ne ya tabbatar da hakan yayin wani taron manema labarai a birnin Abuja, inda ya ce duk da dai mutanen da aka sace an boye su a wurare masu wahalar ganowa cikin sauki, amma duk da haka rundunar sojin kasar za ta yi bakin kokarin ceto su da lafiyar su.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Kamar yadda bayanai suka nuna, a tsakanin jihohin Borno, Kaduna da Sakkwato, sama da mutane dari hudu ne akasarin su dalibai ‘yan bindiga suka sace, lamarin da sojojin suka bayyana da cewa, ramuwar gayya ce a kan kisan manyan jagororin ‘yan bindigan da sojoji suka yi a baya.

Domin ganin an kai ga nasarar aikin ceto mutanen, rundunar sojin ta Najeriya tana tuntubar kasashen duniya domin su ba ta gudummowa ta fuskar tattara bayanan sirri game da ‘yan bindigar da kuma wuraren da suka killace daliban.

“Muna yin amfani da abokanan huldar na kasashen waje, kuma sun ba mu taimakon da suka hada da na bayanan sirri, wanda wannan zai ba mu dama a kan yadda za mu yi maganin wannan mummunan al’amari, an hallaka da yawa daga cikin kwamandojin ‘yan bindigar yayin farmakin da dakarun soji suka kai sansanonin su, a sabo da haka suke son amfani da daliban da sauran mutanen da suka kama a matsayin garkuwa domin su kuma su cigaba da rayuwa.”

Major Janaral Edwar Buba ya sha alwashin cewar, dakarun sojin Najeriya ba za su saurara ba har sai sun kwato mutanen da lafiyar su daga hannun ‘yan bindiga.(Garba Abdullahi Bagwai)