logo

HAUSA

Jihohin Kano da Bauchi za su fara cin gajiyar shirin bankin duniya na samar da filayen kiwo irin na zamani

2024-03-15 09:19:24 CMG Hausa

Bankin duniya ya kulla yarjejeniya tsakaninsa da gwamnatocin jihohin Kano da Bauchi domin samar da filayen kiwo irin na zamani.

A lokacin da wakilan bankin suka ziyarci gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad, sun shaida cewa bankin na duniya zai samar da kauyuka na musamman guda biyu a kowacce jiha da makiyaya za su rinka gudanar da kiwon dabbobinsu a zamanance.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

A cewar wakilan bankin na duniya, shirin samar da filayen kiwon zai gudana ne a daukacin jihohin arewacin Najeriya saboda a wannan sashe ne aka fi fuskantar rigingimu tsakanin makiyaya da manoma sakamakon karancin filayen kiwo da kuma yawancin iyaka da wasu manoma ke yi.

Ko da yake dai a cewar bankin na duniya yanzu wannan shiri zai fara ne da jihohin Kano da Bauchi a matsayin gwaji kafin zuwa lokacin da za a kara fadada shi.

Malam Sunusi Abubakar shi ne jagoran ayarin wakilan bankin duniyar ya yi wa manema labarai karin bayani a game da shirin. 

“Mun zo nan Bauchi domin Bauchi suna cikin jihohin da suke gudanar da wannan al’amari na bankin duniya, mun zo kuma domin aiwatar da shirin tare da wakilan bankin na duniya domin duba yadda za a kyautata ayyukan da jihar ta gudanar a wannan bangare, kuma mun tarar tuni sun samar da kauyen kiwo wanda musamman an yi shi domin rage rigima tsakanin makiyaya da manoma.”

A lokacin da yake jawabin, gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya ce, domin kara kyautata filayen kiwo da gwmnatin jihar ta samar.

“Za mu gina dam-dam kamar guda 100 a jihar Bauchi, sannan za mu gina wasu dam-dam din a irin wadannan wuraren kiwon na musamman da aka samar saboda wurin ba su da ruwan burtsatsai, domin ya kasance ruwan sama za mu ajaye shi yadda shanun za su rinka samu suna sha.”

Shirin samar da filayen kiwon na bankin duniya, yana kunshe ne da gidaje da wurin koyon sana’a da wurin da dabbobi za su rinka cin abinci wanda wannan zai kawo karshe yawan fadace-fadace tsakanin manoma da makiyaya. (Garba Abdullahi Bagwai)