logo

HAUSA

An bude bikin baje kolin kayayyakin gida da na na’urorin wutar lantarki na yau da kullum a nan kasar Sin

2024-03-15 14:12:54 CGTN HAUSA

 

An bude bikin baje kolin kayayyakin gida da na na’urorin lantarki na yau da kullum a birnin Shenzhen na kasar Sin, wanda ke zama daya daga cikin manyan bukukuwa uku a duniya a wannan fanni. Baje kolin da aka bude a jiya Alhamis, mai taken “Kimiya mai fasahar zamani za ta kyautata zamantakewar dan Adam”, ya ja hankalin manyan kamfanoni na duniya fiye da dubu a wannan bangare.

A gun bikin, an baje kolin kayayyakin gida da na’urori fiye da dubu 10, ciki har da firiji da injin wanke tufafi da wayar salula da sauransu, abubuwan da suka bayyana ci gaban da ake samu a wannan bangare.

Abin da ya fi jan hankalin mahalarta bikin shi ne, fasahar kwaikwayon hazikanci da dai sauran fasahohin dake sahun gaba a duniya da ake amfani da su wajen kera wadannan kayayyaki. Mabambanta kamfanoni na gabatar da kayayyakinsu na zamani dake amfani da wadannan fasahohi, wadanda za su biya bukatun rayuwar jama’a a fannoni daban-daban. (Amina Xu)