logo

HAUSA

Matsayin ci gaban rayuwar jama'a ta kasar Sin ta kasance a kan gaba a duniya

2024-03-15 20:47:17 CMG Hausa

Game da matsayin ci gaban rayuwar jama'a ta kasar Sin dake cikin rahoton yanayin ci gaban rayuwar jama'a daga shekarar 2023 zuwa 2024 da hukumar raya kasashe ta MDD ta gabatar, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, matsayin na Sin ta inganta daga maki 0.499 a shekarar 1990 zuwa maki 0.788 a shekarar 2022, inda kasar Sin ta zama kasa ta farko dake kan gaba a wannan fanni, tun bayan an gabatar da matsayin karo na farko a shekarar 1990.

Wang Wenbin ya bayyana cewa, bayan kasar Sin ta fara bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a gida, yawan mutanen da Sin ta fitar daga kangin talauci ya wuce kashi 70 cikin dari bisa na duniya, hakan ya shawo kan matsalar talauci, da cimma burin yaki da talauci na ajendar samun ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030 ta MDD, shekaru 10 kafin cikar wa’adin. Yawan shekarun jama’ar kasar Sin a matsakaicin mataki ya karu zuwa maki 78.2, yawan kudin shigar kowane mutumin Sin a shekara daya ya kai kimanin kudin Sin Yuan dubu 40. Kana Sin ta kafa tsarin ba da ilmi da tabbacin zamantakewar al’umma da kiwon lafiya mafi girma a duniya, jama’ar kasar Sin suna kara jin dadin zaman rayuwa da samun tsaro. (Zainab Zhang)