logo

HAUSA

Shugaban Angola ya ajiye furanni a gaban hasumiyar tunawa da jaruman kasar Sin

2024-03-15 14:14:25 CMG Hausa

Da safiyar yau Jumma’a, shugaban kasar Angola Joao Lourenco, wanda yake ziyarar aiki a kasar Sin, ya je filin Tian'anmen dake birnin Beijing, inda ya ajiye furanni a gaban hasumiyar tunawa da jaruman kasar Sin. 

Bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa, shugaban kasar Angola Joao Lourenco ya iso filin jirgin sama na kasa da kasa na birnin Beijing da safiyar jiya Alhamis, domin fara ziyarar aiki a kasar Sin. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)