logo

HAUSA

Amurka Ta Dade Tana Yada Karairayi Game Da Kasar Sin

2024-03-15 20:23:06 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Amurka ta dade tana yada bayanan bogi game da kasar Sin ta hanyar shafe shekaru tana tsara hanyoyi da dabaru, wadanda suka zama muhimmiyar hanyarta ta yakar kasar Sin.

A cewar kafar yada labarai ta Reuters, tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya rattaba hannu kan wani umarnin sirri a shekarar 2019, wanda ya ba hukumar leken asiri ta CIA iznin kafa wata tawaga ta musamman a kasar Sin da kudu maso gabashin Asiya da kudancin yankin tekun Pacifik da Afrika da sauran wurare, ta hanyar sayen kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta na bogi da sauran wasu boyayyun hanyoyi na yada abubuwan dake shafawa kasar Sin bakin fenti.

Wang Wenbin ya yi wannan bayani ne yayin da yake amsa tambayar wani dan jarida a taron manema labarai na yau Jumma’a. Ya kuma kara da cewa, kitsawa da yada karairayi babu abun da za su yi, illa gaggauta zubar da kimar Amurka. Bugu da kari, ya ce yada bayanan karya ba zai dakatar da Sin daga samun ci gaba ba, amma zai ci gaba da kara zubar da kimar Amurka. (Fa’iza Mustapha)