logo

HAUSA

Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Zai Kai Ziyara Kasashen New Zealand Da Australia

2024-03-14 19:08:57 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a yau Alhamis cewa, bisa gayyatar mataimakin firaminista kuma ministan harkokin wajen kasar New Zealand Winston Peters, da ministar harkokin wajen kasar Australia Penny Wong, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, zai ziyarci kasashen New Zealand da Australia daga ranar 17 zuwa 21 ga wata.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin ne ya sanar da hakan, inda ya ce yayin ziyarar ta Wang Yi, zai gudanar da tattaunawa karo na 7 tsakanin Sin da Australia tare da takwararsa ta kasar, Penny Wong dangane da harkokin waje da manyan tsare-tsare. (Fa’iza Mustapha)